Logo
AbubakarImam.com
Logo
|

All Files

  Free Adobe Reader You may download and use Adobe Reader to read the digital eBooks. It's simple to use and it's free! Adobe Reader
  To Download eBook Click or Right Click on Download and choose 'Save Target As'!

Viewing: Magana Jarice 1

Magana Jarice 1 9027 Downloads

Magana Jarice 1 Magana Jarice 1
Published By: NNPC
Date Published: 1937
ISBN: 978-169-057-7

Wannan littafi, Magana Jari Ce, 1, yana cikin littattafai guda uku da Alhaji Abubakar Imam ya rubuta a cikin wata shida na zamansa a Zariya a shekarar 1936. Dalilin zabo shi kuwa ya rubuta wadannay littattafai shi ne ya shiga wata gasa to rubutun littafi a sheka rar 1933 ya kuma ci nasara da littafinsa na farko 'Ruwan Bagaja'.

An haifi Alhaji Dr. Abubakar Imam, O.B.E; C.O.N.; LL.D (Hon.) N.N.M.C. a shekarar 1911 a cikin garin Kagara sa'an nan tana cikin lardin Kwantagora, yanzu kuwa Jihar Neja. Ya yi makaranta a Katsina Training College kuma ya kama aikin malanta a Makarantar Midil to Katsina a shekarar 1932. Yana da shekara 22 ya rubuta 'Ruwan Bagaja'. Ganin kwazonsa wajen Raga labari mai ma'ana ya sa Dr. R. M. East shugaban Offishin Talifi na Zariya ya roki a ba da shi ato daga Katsina ya yi aikin rubuce rubuce a Zariya.

Bayan ya koma Katsina aka bi shi da rokon ya kara rubuta wasu littattafan. A can ya rubuta 'Karamin Sani kukumi' cikin 1937. A cikin shekara 1938 sai Gwamnan Kaduna ya roka a dawo da Imam Zariya a koya mashi aikin edita ya zama editan jaridar farko to Arewa. Shine ma ya rada mata suna `Gaskiya Ta Fi Kwabo' aka fara bugawa a watan Janairu na shekara 1939.

Ya yi shekara 12 yana wannan aiki na edita har ma ya rubuta wani littafi a lokacin 'Yakin Duniya Na Biyu' watau `Yakin Hitila' da ya ba suna 'Tafiya Mabudin Ilmi'. Wannan littafi ya ba da labarin tafiyarsa tare da wasu editoci na jaridun Africa to Yamma zuwa Ingila a jirgin ruwa a shekara 1943.

Wani mashahurin littafi kuma da ya rubuta shi ne 'Tarihin Annabi da na Halifofi' wanda aka fara buga shi a shekara 1957 lokacin nan yana shugaban Hukumar Daukar Ma'aikata to Nijeriya to Arewa.

Alhaji Dr. Abubakar Imam shi aka fara nadawa Kwamishinan Jin Kararakin Jama'a a shekara 1974 a Jihar Kaduna, lokacin ana kiranta Arewa to Tsakiya. Ya rasu yana da shekara 70 a duniya ranar Juma'a 19 ga watan Yuni, 1981.

Alhaji Abubakar Imam ya rika cewa wannan aiki da ya yi, na talifin 'Magana Jari Cc' ya yi masa amfani ainun. Ya kan cc wannan aiki shi ne ya ba shi damar zama tare da mashahurin Baturen nan na talifin Hausa, Dr. R. M. East, O.B.E. Ya cc daga gare shi. ne ya koyi duk dan abin da ya koya na game da talifi.

Abin mamaki, shi kuma wannan Bature, Dr. East O.B.E., a wajen `Mukaddamar' da ya yi da Turanci tun farkon buga 'Magana Jari Ce', ga abin da ya ce : 'Muna godiya ga En'e to Katsina, saboda taimakonsu, da hangen nesa da suka yi, har suka yarda, suka ba mu aron Malam Abubakar Imam. Suka yarda, ya bar aikinsa, na koyad da Turanci a Midil to Katsina, ya zo nan Zariya, ya yi wata shida domin ya taimake mu, mu sami wadannan littattafai a cikin harshensa.

`lyakar abin da mu ma'aikatan wannan ofis muka yi, na game da talifin wadannan littattafai, shi ne aiki irin na ofis, na shirya al'amuran, yadda suka kai har aka buga su. Ban da wannan sai kuma taimakonsa da muka yi na tattara masa littattafai iri iri, don ko zai kwaikwayi wani samfur. Sai fa, kuma wajen shiryawa bayan da ya rubuta.

'Kai, in dai har muna da wani abin da za mu yi kirari mun yi, .game da talifin wadannan littattafai, to, babban abin kirarimmu kawai, shi ne yadda muka yi har muka binciko wannan malamin talifi'.

1982

N.N.P.C.




Date: 22/10/2004 Filesize: 5422KB

File Toolbox

Comments

Kai an gaisheku! Wannan fajin yayi.

Posted By: Salisu U. Danyaro on 10/11/2004 at 14:56:24

Assalamu alaikum, i'm very happy when i come across this site. Dr Abubakar books are my best. I never get tied of reading them.Now that i'm far from Nigeria, i couldn't lay my hand on the books. You are doing a good job & you are showing the best of north. keep it up &Allah bless you.

Posted By: Nuwaira Abdullah Idris on 14/03/2005 at 4:55:00

'Magana Jari ce' lalle magana jari ce. Don kuwa dukkan labarai da saitin littattafan uku suka kunsa sum zama abin koya kwazo, hankali, dabi-o-i, wasiya, da tarihi. Allah ya jikan Marigayi Mallam Abubakar Imam, ya kuma bamu kwatanta kwazonsa. Godiya ta musamman ga wadanda suka shirya wannan shafi, da bada damar samun littafin ta 'internet' (a rashin fassara a hausance).

Posted By: Mohammed Ali on 15/03/2005 at 9:14:04

Kai amma naji dadi dangane da wannan aiki naku, Allah ya saka da alkairinsa ya kuma kara basira sosai.
Sai dai kuma zanso ace kunyi kokari wajen ganin wannan abu yaci gaba domin ci gabane garemu baki day (ina nufin hausawanmu da kuma wadanda ba hausawaba ma) domin hakan na iya karawa yaran wani kwarjini a idanun duniya musamman a wannan zamani na gasar wayewa ta harkoki dabam-dabam.
kuma don Allah ayi kokari wajen ganin an fassara littattafan marigayi izuwa sauran harsuna domin duniyar zamanin nan taga irin gwarzon aikin da yayi wa al'ummarsa.
MA'ASSALAM,

Posted By: Ya'aqoub Abdul-Hameed on 06/05/2005 at 12:11:44

Yaka mata a sa tafiya mabudin ilimi a website kuma a buga shi ya shiga kasuwa don mutanesuna da bukatarsa kwarai da gaske.

Posted By: Munzli U. Gama on 12/05/2005 at 14:00:15

assalamu alaikum, don Allah ina son in san yanda zan sami izini don karanta wannan labari na magana jarice a gidan rediyon ray power kano. sun bani dama amma sai na sami izini daga NNPC. don Allah a sanar dani abin yi. domin ni wannan littafi ya taimaka ma zaman rayuwata a duniya. dan haka na ke son sauran yara da jama'a su amfana. kuma wannan site zan sanar da jama'a shi ta cikin shirin.

08054724860
musa sufi kano

Posted By: musa abdullahi sufi on 15/07/2006 at 12:40:16

allah sarki allah yajikan! mallam arewa musulmi da kirista, sunyi rashin mallam wanda har gobe ake tunashi. munufar mallam bazamu iya kwatanta ta ba ba wani sai kai! ba aiba bakuma za ai ba, allah yasaka maka da aljannarsa mallam amin muma muna zuwa sai munzo !

Posted By: habu jikau on 28/11/2006 at 19:49:02

allah sarki allah yajikan! mallam arewa musulmi da kirista, sunyi rashin mallam wanda har gobe ake tunashi. munufar mallam bazamu iya kwatanta ta ba ba wani sai kai! ba aiba bakuma za ai ba, allah yasaka maka da aljannarsa mallam amin muma muna zuwa sai munzo !

Posted By: habu jikau on 28/11/2006 at 19:49:29

allah sarki allah yajikan! mallam arewa musulmi da kirista, sunyi rashin mallam wanda har gobe ake tunashi. munufar mallam bazamu iya kwatanta ta ba ba wani sai kai! ba aiba bakuma za ai ba, allah yasaka maka da aljannarsa mallam amin muma muna zuwa sai munzo !

Posted By: habu jikau on 28/11/2006 at 19:51:52

this is a good work,it will help the young writers and the present generation especially in hausa literature.

Posted By: usman abdallah on 13/01/2007 at 10:57:38

Pages

Page - 1 - 2