Logo
AbubakarImam.com
Logo
|

All Files

  Free Adobe Reader You may download and use Adobe Reader to read the digital eBooks. It's simple to use and it's free! Adobe Reader
  To Download eBook Click or Right Click on Download and choose 'Save Target As'!

Viewing: Magana Jari Ce 3

Magana Jari Ce 3 28955 Downloads

Magana Jari Ce 3 Magana Jari Ce 3
Published By: NNPC
Date Published: 1939
ISBN:

Wannan littafi, `Magana Jari ce, 3', yana cikin littattafai guda uku da Alhaji Abubakar Imam ya rubuta a cikin wata shida na zamansa a Zariya a shekarar 1936. Dalilin za6o shi kuwa ya rubuta wadannan littattafai shi ne ya shiga wata gasa to rubutun littafi a shekarar 1933 ya kuma ci nasara da littafinsa na farko 'Ruwan Bagaja'.

An haifi Alhaji Dr. Abubakar Imam, O.B.E; C.O.N.; LL.D (Hon.) N.N.M.C. a shekarar 1911 a cikin garin kagara sa'an nan tana cikin lardin Kwantagora, yanzu kuwa Jihar Neja. Ya Yi makaranta a Katsina Training College kuma ya kama aikin malanta a Makarantar Midil to Katsina a shekarar 1932. Yana da shekara 22 ya rubuta `Ruwan Bagaja'. Ganin kwazonsa wajen Raga labari mai ma'ana ya sa Dr. R.M. East shugaban Offishin Talifi na Zariya ya roki a ba da shi aro daga Katsina ya yi aikin rubuce rubuce a Zariya.

Bayan ya koma Katsina aka bi shi da rokon ya kara rubuta wasu , littattafan. A can ya rubuta 'Karamin Sani kukumi' cikin 1937. A cikin shekara 1938 sai Gwamnan Kaduna ya roka a dawo da Imam Zariya a koya mashi aikin edita ya zama editan jaridar farko to Arewa. Shi ne ma ya rada mata suna `Gaskiya Ta Fi Kwabo' aka fara bugawa a watan Janairu na shekara 1939.

Ya yi shekara 12 yana wannan aiki na edita har ma ya rubuta wani littafi a lokacin `Yakin Duniya Na Biyu' watau `Yakin Hitila' da ya ba suna `Tafiya Mabudin Ilmi'. Wannan littafi ya ba da Iabarin tafiyarsa tare da wasu editoci na jaridun Africa to Yamma zuwa Ingila a jirgin ruwa a shekara 1943.

Wani mashahurin littafi kuma da ya rubuta shi ne 'Tarihin Annabi da na Halifofi' wanda aka fara buga shi a shekara 1957 lokacin nan yang shugaban Hukumar Daukar Ma'aikata to Nijeriya to Arewa.

Alhaji Dr. Abubakar Imam shi aka fara nadawa Kwamishinan Jin Kararakin Jama'a a shekara 1974 a Jihar Kaduna, lokacin ana kiranta Arewa to Tsakiya. Ya rasu yana da shekara 70 a duniya ranar Juma'a 19 ga watan Yuni, 1981.

Alhaji Abubakar Imam ya rikca cewa wannan aiki da ya yi, na talifin 'Magana Jari e' ya yi masa amfani ainun. Ya kan ce wannan aiki shi ne ya ba shi damar zama tare da mashahurin Baturen nan na talifin Hausa, Dr. R.M. East, O.B.E. Ya ce daga gare shi ne ya koyi duk dan abin da ya koya na game da talifi.

Abin mamaki, shi kuma wannan Bature, Dr. East O.B.E., a wajen `Mukaddamar' da ya yi da Turanci tun farkon buga 'Magana Jarice, ga. abin da ya ce : 'Muna godiya ga En'e ta Katsina, saboda taimakonsu, da hangen nesa da suka yi, har suka yarda,suka La wu anon Malam Abubakar imam. sutra yarda, ya bar aikinsa, na koyad da Turanci a Midil to Katsina, ya zo nan Zariya, ya yi wata shida domin ya taimake mu, mu sami wadannan littattafai a cikin harshensa.

`Iyakar abin da mu ma`aikatan wannan ofis muka yi, na game da talifin wadannan littattafai, shi ne aiki irin na ofis, na shirya al'amuran, yadda suka kai har aka bugs su. Ban da wannan sai su kuma taimakonsa da muka yi na tattara masa littattafai iri iri, don ko zai kwaikwayi wani samfur. Sai fa kuma wajen shiryawa bayan da ya rubuta.

'Kai, in dai har muna da wani abin da za mu yi kirari mun yi, game da talifin wadannan littattafai, to, babban abin kirarimmu kawai, shi ne yadda muka yi har muka binciko wannan malamin talifi'.

1982

N.N.P.C.
Date: 10/11/2004 Filesize: 9943KB

File Toolbox

Comments

Ia m honoured to say a word about this litrary genius whose writings has touch an infinite nunmber of souls. The best could be said of him are prayers. May Allh reward him abundantly, Ameeen.

Posted By: Engr Saidu A. Hamdullahi on 15/03/2005 at 3:20:15

'Magana Jari ce' lalle magana jari ce. Don kuwa dukkan labarai da saitin littattafan uku suka kunsa sum zama abin kwazo, hankali, dabi-o-i, wasiya, da tarihi. Allah ya jikan Marigayi Mallam Abubakar Imam, ya kuma bamu kwatanta kwazonsa.

Posted By: Mohammed Ali on 15/03/2005 at 9:08:22

There is no doubt the lessons from Dr. Imam's writing have help tranformed me into a better person. I have read and told his stories to many people and I am absolutely sure they have benefitted a lot from that as well. May his soul rest in perfect peace, ameen.

Posted By: Abu Sani on 04/04/2005 at 22:56:45

There is no doubt the lessons from Dr. Imam's writing have help tranformed me into a better person. I have read and told his stories to many people and I am absolutely sure they have benefitted a lot from that as well. May his soul rest in perfect peace, ameen.

Posted By: Abu Sani on 04/04/2005 at 22:57:28

This is the best literary work ever done to potray the Hausa culture and tradition to the entire world.

Posted By: Usman Leman on 18/07/2005 at 3:37:54

Allah yajikan marubuci Allah kuma yasa yacikada imani amin damuna da irisa ahalin da muke ciki ayanzun da harshen hausa bai lalaceba sai dai muce Allah yajikan maza

Posted By: Aliyu sambo supreme court of Nig. on 28/07/2005 at 10:25:52

i am happy for this important
contribution to our hausa culture.

Posted By: hussein muhd on 16/12/2005 at 7:53:36