Logo
AbubakarImam.com
Logo
|

All Files

  Free Adobe Reader You may download and use Adobe Reader to read the digital eBooks. It's simple to use and it's free! Adobe Reader
  To Download eBook Click or Right Click on Download and choose 'Save Target As'!

Viewing: Ruwan Bagaja

Ruwan Bagaja 9711 Downloads

Ruwan Bagaja Ruwan Bagaja
Published By: NNPC
Date Published: 1934
ISBN:

A cikin farkon zamanin Shaihu dan Ziyazzinu an yi wani mutum motsatstse, wanda a ke kira Koje Sarkin Labari. Dalilin da ya sa a ke kiransa haka, don haukansa ba na zagin kowa ba ne,bakuwa na dukan kowa ba ne. Shi dai ba abin da ya ke so sai ya ji labari, ya tafi wadansu kasashe, ya rika ba attajirai da Sarakuna, su kuwa suna ba shi abinci. In ya ba ka labari, wanda ba ka sani ba, in ka ba shi kudi, sai ya debi hams ya ba ka. Ya tsare ka, ya ce kai kuma sai ka ha shi wani labari, wanda shi kuma bai sani ba.

Yana cikin bin kasashe, har ran nan Allah ya sa ya isa wani gari wai shi Kwantagora, wani babban birni ne a cikin kasar Sudan. Ya isa wajen Sarkin garin, aka kai shi masauki. Da ajiye kayansa, sai ya fito kofar fada, ya shiga halinsa na neman labaru da ba da su. Ya kwana kamar uku yana ba Sarki labarurruka, fadawa kuwa suna biyansa da wadansu labaru, watau maimakon wad'anda ya ba Sarkinsu. Sarkin kasar ana kiransa Sarkin Sudan.

Yana yawo cikin gari, sai ya isa wani Raton gida mai benaye da yawa. Ya tambayi barorin da ya tarar zaune ya ce, "Shin gidan wane ne wannan ?"

Suka ce, "Wane ne duk duniyan nan bai san Alhaji Imam ba ?"

Koje Sarkin Labari ya ce musu, "Yana fitowa yanzu ?" Suka ce, "Wa zai fito da shi yanzu tun azahar ba to yi ba ?" Koje ya share wuri, ya zauna kan azahar to yi.

Azahar na yi, sai suka ji taf, taf, duk zaure aka tashi. Da maigida ya shigo aka fadi aka yi gaisuwa. Da ya zauna ya dubi Koje ya ce, "Wannan fa wane ne ?"

Koje ya ce, "Ni ne Sarkin Labari. Yau kwanana goma nan garin. Ka ji ka ji safarata ka kuwa ji yadda a ke biyana, ko kana iya saye ?"




Date: 10/11/2004 Filesize: 2005KB >

File Toolbox

Comments

wannan yana daga cikic littattafan da babu irinsu a duniya. lallai imam ya yi kokari a wajen rubuta shi

Posted By: muhammad lawal abubakar on 13/11/2004 at 2:37:30

Allah yaji kan Dr. Abubakar Imam. dukkan littattafansa suna maana da dadin karantawa.

Posted By: abba hamza on 07/12/2004 at 21:58:24

one of the greatest scholars ever produced by the country whose role cannot be replaced by the invent of present times.

Posted By: Abubakar Imam on 11/12/2004 at 15:55:32

sawerf

Posted By: muhammed on 25/02/2005 at 8:44:23

Allah ya jikan Dr. Abubakar Imam ya gafarta mashi. a gaskiya wannan littafi na ruwan Bagaja yan daya daga cikin litattafai da tarihi ba zaya tafa mantawa dasu ba a kasar hausa don kuwa yayi ma'ana. Lalai Alhaji yayi kokari,
ina fatan marubuta litattafai na hausa a wannan zamani zasu yi koyi da Alhaji.

Posted By: Abubakar kafin Soli Usman on 14/03/2005 at 8:19:03

Hakika Mallam Abubakar Imam ya kasance mai Hazaka wajen tsara lissafin wannan littafin, cike da ma'ana, annashuwa, da darussa. Saidai muce, Allah jikan Mallam ya bamu ikon amfani da ilminsa. Godiya ga tsara wannan shafi.

Posted By: Mohammed Ali on 15/03/2005 at 8:56:15

Allah ya sakawa jagoran marubuta littafan hausa da alheri domin tarihin rubun hausa a duniya ba zai manta da Alhaji abubakar imam ba Allah ya jikansa yasa ya huta

Posted By: zahir sulaiman abaya on 17/03/2005 at 9:00:33

wannan yana daga cikic littattafan da babu irinsu a duniya. lallai imam ya yi kokari a wajen rubuta shi

Posted By: muhammad lawal abubakar

Posted By: bdulykasaiy2k on 13/07/2005 at 10:16:39

Babu kamar wannan littafi a halinyanzun sai dai muce Allah yajikan marubucin amin.

Posted By: Aliyu sambo supreme court of Nig. on 28/07/2005 at 10:34:29

Assalamu alaikum. Ina ci gaba da bayyana farin cikina da ganin wannan shafin da aka bude shi, musamman domin Malam Abubakar Imam. Hakika bude wannan shafin zai karfafawa ba kawai mu kananan marubuta masu tasowa ba, amma har zai kara wayar da kan manya, kuma tsaffin marubuta da suka dade a wannan harkar ta rubuce-rubuce. Fatan da nake da shi kawai shi ne, Allah ya ba wadanda suka dakko wannan dalar ba gammo damar sauke ta a cikin kwanciyar hankali da lumana. Ina fatan za a ci gaba da sanya sabbin abubuwa a wannan shafin ba wadanda kawai suka shafi Marigayi Malam Imam ba, amma har ma da abubuwan da suka shafi al'ummar Hausawa da kuma shi kansa yaren na Hausa baki daya. Allah ya yi taimako, ya kara maku karfin giwa, amin.
Aliyu Saleh, Editan Labarai na jaridar Almizan da ake bugawa a Babban Dodo, Zariya jihar Kaduna

Posted By: Aliyu Saleh on 08/08/2005 at 3:08:24

Pages

Page - 1 - 2